Birnin Tarihi na Ahmadabad

Birnin tarihi na Ahmadabad ko Tsohon Ahmedabad, birni mai katanga na Ahmedabad a Indiya, Ahmad Shah I na Gujarat Sultanate ne ya kafa shi a shekara ta 1411. Ya kasance babban birnin Sultanate Gujarat kuma daga baya muhimmiyar cibiyar siyasa da kasuwanci ta Gujarat. A yau, duk da kasancewar cunkoson jama'a da rugujewa, har yanzu tana zama alamar zuciyar dan birni Ahmedabad. UNESCO ta sanya shi a matsayin Garin Tarihi na Duniya a cikin Yulin shekarar 2017.


Developed by StudentB